Rasha Ta Jaddada Kin Amincewa Da Yakar Kasar Ira

, minstan harkokin wajen Iran ya yabawa Rasha saboda matsayarta akan harin wuce gona da iri na Amurka akan Iran,tare da cewa rashin tsaron da
ganawar araghchi da Lavrov

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci da halarci taron kungiyar Shanghai a kaar Kyrkizystan ya gana da takwaransa na kasar Rasha Sergey Lavrov

A yayin ganawar tasu, bangarorin biyu sun tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakanin kasashen nasu a bangarorin siyasa, tattalin arziki, kasuwanci, sufuri da kuma makamashi.

Haka nan kuma bangarorin biyu sun tattaun yadda kasashen nasu za su aiwatar da yarjeniyoyin da su ka rattaba hannu akansu a baya.

A nashi gefen, minstan harkokin wajen Iran ya yabawa Rasha saboda matsayarta akan harin wuce gona da iri na Amurka akan Iran,tare da cewa rashin tsaron da ake fama da shi a wannan lokacin a yankin Hurmuz, sakamakonsa keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta yi ne.

Shi kuma Lavrov ya sake jaddada matsayar kasarsa na kin amincewa da harin wuce gona da iri na Amurka da Isra’ila akan Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted