IRGC Sun Kira Yi Mutanen Da Su Kauracewa Zama Kusa Da Mabuyar Sojojin Amurka Da Tazarar Mita 500

IRGC Sun Kira Yi Mutane Da Su Kauracewa Zama Kusa Da Mabuyar Sojojin Amurka Da Tazarar Mita 500 saboda kare lafiyarsu
dakarun kare juyin musulunci na Iran

Bangaren hulda da jama’a na dakarun kare juyin musulunci ta Iran  ( IRGC) ya fitar da sanarwa da a ciki ya kira mutanen da suke a cikin kasashen da Amurka take da sojoji da su kaucewa mabuyar sojojin ”yan ta’adda na Amurka da tazarar mita 500.”

Sanarwar ta fara da cewa:

“Watanni biyar da su ka gabata, gwamnatin Amurka mai kashe kananan yara sun shelanta yaki akan kasarmu ba tare da wani dalili na hankali ko doka ba, su ka kashe babban malamin addini kuma jagora na siyasa, a lokaci daya kuma su ka kashe kananan yara 168 ba tare da wani dalili ba.”

Haka nan kuma dakarun kare juyin sun ce; Bisa la’akari da cewa ci gaba da tafaka wadannan laifukan da Amurkawa suke yi, daukar fansa akansu ya zama wajibi. Kuma da dama daga cikin sojojin na Amurka an dauke su daga sansanoninsu zuwa Mabuya saboda tsoron mujahidin musulunci, suna rayuwa a cikin gari domin ci gaba da tafiyar da laifukansu, to don haka muna yin kira ga dukkanin ‘yan kasashen da Amurka take da sansanoni a cikinsu, da su gagauta nesantar wadannan wuraren da tazarar mita 500, domin kare lafiyarsu.”

Bugu da kari,muna yin kira ga ‘yan kasa da su aiko mana da bayani akan irin wadannan wuraren da sojojin na Amurka su ka buya a cikinsu ta hanyar telegram ko kuma ta hanyoyin saduwa da mu ta internet.

Wani sashe na sanarwar dakarun kare juyin ya kunshi cewa yakin kwanaki 40 Iran ce ta sami nasara, amma kuma duk da haka Iran din ta amince da dakatar da yaki, tare da cewa za ta iya ci gaba da yakin, saboda samar da zaman lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted