Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas sun sanar da cewa: ‘Yan gwagwarmayar kungiyar sun tarwatsa wata motar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila da wani makami mai linzami lamarin da ya yi sanadin halakar sojojin da suke ciki tare da tashin gobara a cikin motar a yankin tsakiyar Bani Suhaila da ke gabashin birnin Kham Yunus.
Har ila yau, Dakarun na Al-Qassam sun bayyana cewa: ‘Yan gwagwarmayarsu sun kai harin kwanton bauna kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a garin Jenin da ke yammacin gabar kogin Jordan, a washegarin shahadar wasu jagororinsu uku a garin Tulkaram.
Kamar yadda dakarun sojin Izzuddeen Al-Qassam suka jaddada cewa: Mayakansu sun kai wasu hare-haren kwantan bauna har sau uku kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a kusa da kauyen Al-Matula, dake daura da birnin Jenin, lamarin da ya yi sanadin jikkatar sojojin yahudawan sahayoniyya ciki har da wani babban jami’insu, tare da tabbatar da cewa ‘yan gwagwarmayar da suka kai hare-haren sun janye lami lafiya.