Yan Gwagwarmayar Falasdinu Sun Jaddada Aniyarsu Ta Ci Gaba Da Yaki

Rundunar Izzul-Din al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada shirinta na ci gaba da yaki A wani faifan bidiyo da ta watsa

Rundunar Izzul-Din al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada shirinta na ci gaba da yaki

A wani faifan bidiyo da ta watsa a jiya Alhamis, Rundunar Izzul-Din al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada shirinta na ci gaba da yaki da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, tana mai fayyace cewa: Dakarunta a shirye suke su rusa martabar rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila sakamakon yadda mayakanta suke sa-ido da shirye-shiryen harba makamai masu linzami kan sassa daban-daban na haramtacciyar kasar Isra’ila.

Wannan gargadi na rundunar Izzuddeen Qassam yana zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojin yahudawan sahayoniyya suke ci gaba luguden wuta kan birnin Rafah da ke kudancin Zirin Gaza, lamarin da kungiyar Hamas ta jaddada cewa; Wannan barna ba za ta wuce ba tare da mayar da martani mai tsanani ba, kuma haramtacciyar kasar Isra’ila zata kwashi kashinta a hannu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments