Kafofin yada labaran Isra’ila: Masar ta yi barazanar soke yarjejeniyar Camp David da Isra’ila

Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayar da rahoton barazanar da Masar ta yi wa Isra’ila na soke yarjejeniyar Camp David idan ba ta dakatar da ayyukanta a birnin Rafah ba, tare da jaddada wajabcin komawa ga tattaunawa mai tsanani. Jaridar “Maariv” ta kasar Isra’ila ta tabbatar da cewa jami’an Masar sun sanar da daraktan hukumar […]
UNRWA Ta Rufe Hhedikwatarta A Quds Sakamakon Hare-haren Yahudawa

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Falasdinu UNRWA ta rufe hedikwatarta da ke gabashin birnin Quds bayan da ‘yan Isra’ila mazauna yankin suka cinna wuta a kewayen ginin a gaban dakarun gwamnatin kasar. Shugaban hukumar ta UNRWA Philippe Lazzarini ya fada a ranar Alhamis cewa, “A yammacin yau, mazauna Isra’ila sun cinna wuta sau […]
Netanyahu : Biden Ya Tafka Kuskure Wajen Dakatar Da Bai Wa Isra’ila Makamai

Jami’an Isra’ila na ci gaba da raddi wa shugaban kasar Amurka Joe Biden wanda ya yi gargadin cewa Amurka ba za ta samar da makaman da Isra’ila za ta kai a gagarumin farmaki a kudancin Gaza da ke birnin Rafah, inda dubban daruruwan Falasdinawa ke gudun hijira. Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya fada a wani […]
Chadi : Mahamat Idriss Deby Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Da Sama Da Kashi 61%

Hukumar zaben kasar Chadi ta ayyana cewa shugaban kasar na rikon kwarya Janar Mahamat Idriss Deby Itno ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 6 ga watan Mayu da sama da kashi 61% na jimillar kuri’un da aka kada. Shugaban Hukumar Zaben Ahmed Bartichet ya fada a ranar Alhamis cewa Deby […]
Ana Zaben Cike Gurbi Na ‘Yan Majalisar Dokoki A Iran

A Iran, yau ake kada kuri’a a zaben neman cike gurbi na ‘yan majlaisar dokokin kasar, domin tantance makomar kujeru 45 da suka rage a majalisar mai wakilai 290. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kada kuri’arsa a safiyar yau Juma’a a farkon bude rumfunan zabe zagaye na biyu na zaben ‘yan majalisar dokokin zagaye […]
Cikan Kwanaki 216 Da Fara Yakin Kisan Kiyashi A Zirin Gaza Na Falasdinu

An cika kwanaki 216 da fara kisan kiyashi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila take yi a Zirin Gaza na Falasdinu Sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da aikata laifukan kisan kiyashi a Zirin Gaza, a rana ta 216 a jere, ta hanyar kai hare-hare da dama ta sama da kasa da kuma harba makaman […]
Yan Gwagwarmayar Falasdinu Sun Jaddada Aniyarsu Ta Ci Gaba Da Yaki

Rundunar Izzul-Din al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada shirinta na ci gaba da yaki A wani faifan bidiyo da ta watsa a jiya Alhamis, Rundunar Izzul-Din al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada shirinta na ci gaba da yaki da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, tana mai fayyace cewa: […]
Amurka Ta Gargadi Babban Lauya Mai Shigar Da Kara A Kotun Kasa Da Kasa

Amurka ta yi barazana ga babban lauya mai shigar da kara a kotun kasa da kasa ta ICC cewa zai fuskanci mayar da martani, idan har ya fitar da sammacin neman kama jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila Mambobin majalisar dattijan Amurka sun yi barazana ga mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya […]
Kungiyar Al-Nujaba’u Ta Kasar Iraki Ta Yi Alkawarin Kai Hari Tsakiyar Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Kungiyar gwagwarmaya ta Al-Nujaba’u ta yi alkawarin kai zafafan hare-haren daukan fansa kan muhimman wurare a haramtacciyar kasar Isra’ila A martanin da kungiyar gwagwarmayar kasar Iraki ta Al-Nujaba’u ta fitar a jiya alhamis ta yi alkawarin mayar da martani mai tsanani da zai kasance na bazata tare da yin mummunan tasiri kan gwamnatin haramtacciyar kasar […]
Hukumar Zaben Kasar Chadi Ta Fitar Da Sakamakon Zaben Shugaban Kasar

Hukumar zaben Chadi ta sanar da nasarar Mohamed Idriss Deby a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa Hukumar zabe ta gwamnati a kasar Chadi a jiya Alhamis ta fitar da sanarwar cewa: Shugaban kasar na rikon kwarya Mohamed Idriss Deby ya lashe zaben shugabancin kasar da aka gudanar a ranar 6 ga watan Mayu […]