‘Yan Ci-Rani 89 Ne Suka Halaka A Gabar Tekun Mauritaniya Bayan Kifewar Kwale-Kwalensu

‘Yan ci-rani ba bisa ka’ida ba 89 ne suka mutu bayan kwale-kwalen da suke ciki ya nutse a gabar tekun Mauritaniya Kamfanin dillancin labaran kasar

‘Yan ci-rani ba bisa ka’ida ba 89 ne suka mutu bayan kwale-kwalen da suke ciki ya nutse a gabar tekun Mauritaniya

Kamfanin dillancin labaran kasar Mauritania ya sanar da cewa: A karshen makon da ya gabata, bakin haure 89 da suka mutu, yayin da wasu da dama suka bace bayan da kwale-kwalen da suke ciki ya nutse a gabar tekun kasar Mauritaniya a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Turai ta hanyar teku ba bisa ka’ida ba.

Kamfanin dillancin labaran ya jiyo wani babban jami’in tsaron gabar tekun Mauritaniya da ya nemi a sakaye sunansa yana cewa: Rundunar tsaron gabar tekun Mauritaniya ta samu nasarar gano gawarwakin bakin haure 89 da ke cikin wani babban kwale-kwalen kamun kifi na gargajiya da ya nutse a ranar Litinin 1 ga watan Yuli a nisan kilomita 4 daga birnin Engago.

A cewar rahoton, wadanda suka tsira daga cikin bakin hauren sun ce, jirgin ya taso ne daga kan iyakar kasashen Senegal da Gambia dauke da fasinjoji 170, wanda ya janyo adadin mutanen da suka bata suka kai zuwa kusan mutane 72.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments