Rundunar sojojin Amurka 5th Fleet a kasar Bahrain na daga cikin wuraren da rundunar IRGC da kuma sojojin kasar Iran suka kaiwa hare-hare a dare na 3 a jere da suke fafatawa da sojojin kasar Amurka a kudancin kasar Iran.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto IRGC da kuma sojojin kasar suna bada wannan labarin a safiyar yau Alhamis, rundunonin 2 sun maida mmartani ne kan sojojin Amurka bayan hare-haren da suka kaiwa wasu wurare a kudancin kasar, wadanda suka hada da wuraren aikin jami’an tsaro nab akin ruwan tekun farisa, tashar jiragen sama na Bandar Abbas da sauransu.
Labarin ya kara da cewa rundunar IRGC da kuma sajojin makamai masu linzami da kuma na ruwa, sun maida martani kan wurare 18 na sojojin Amurka a yankin, wadanda suka hada da sansanin sojojin Amurka mai suna Ali Al-Salem da kuma Ahmad Al-Jaber da suke kasar Kuwait, da kuma sansanin sojojin Amurka na Sheikh Isa da ke Bahraine.
Sai kuma kakakin sojojin Iran ya ce sun yi amfani da makaman Drones a kan rundunar Amurka ta 5Th da ke kasar Bahrain.
Sannan a wani labarin kuma a safiyar yau Alhamis ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya ce ya tsaida wuta a yakin da suke fafatawa da Iran a cikin kwanaki 3 da suka gabata, saboda wai wasu jami’an gwamnatin Iran sun kirashi sun bukaci yayi hakan, amma gwamnaton Iran ta musanta labarin, sun kuma bayyana cewa yayi kariya ne don gudu daga yakin.