Dakarun sojin kasar yamen sun kaddamar da hari kan tankar mai fantur din kasar saudiya a tekun bahar maliya a mashigar ruwa ta Yanbu, a wani mataki na mayar da martani kan hare haren da kasar saudiya ke kai musu da kuma killacewar da ta yi wa kasar yamen
A wani bayani da kakakin sojin kasar yamen birgediya janaral yahya Saree yayi a gidan talabijin din kasar a jiya litinin ya bayyana cewa an kai hari kan tankar mai ta Azman na kasar Saudiya da makami mai linzami na Balistic dake kan hanyarsa a arewacincin tekun bahar maliya.
Hak zalika dakarun sojin kasar yamen sun kai hare- hare daban daban da makami mai linzami na balsitic kan tawagar sojojin kasar saudiya a lokacin da suke tafiya a iyakar al-wadiah dake gabashin hadaramaut, yankin wadiah shi ne babban iyakar da ake shiga saudiya daga kasar yamen
Daga karshe ya nuna cea dakarun sojin kasar ta yamen sun kai hari kan dakarun sojin kasar saudiya a yankin al-kana’is dake yankin Marib da jiragen sama mara matuki , kuma wasu kwamandojin sojojin saudiya sun mutu wasu da dama kuma sun jikkata kuma sun tarwatsa makamai masu yawa dake sansani da yamen take hari