Kakakin majalisar shawara ta kasar Iran mohammad Baqeer qalibaf ya bayyana cewa kasashen iran da Iraqi suna ada muhimmiyar rawa da za su taka wajen samar da sabon tsari a yankin,yana mai jaddada cewa Amurka ta shan kaye a bangaren soji da siyasa a yakin da take yi da kasar Iran,
Da yake bayani a wajen wani babban taro da aka gudanar a nan birnin Tehran da Faeq Zidan shugaban majalisar koli ta shariya ta kasar Iraqi , Qalibaf ya jaddada cewa akwai kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasahen biyu mai dogon tarihi da kuma sauyin yanayin siyasa na yammacin Asiya
qalibaf yace Amurka ce ta fara wannan yaki kan kasar Iran da mummunan nufin kifar da gwamnatin kasar domin ci gaba da fadada Ikonta a fadin kasashen musulmi, sai dai hakarta bata cimma ruwa ba, A nasa bangaren Zidan ya isar da sakon nuna goyon bayan gwamnatin kasar Iraqi ga alumma da gwamnatin kasar iran game da jajircewar da suka ya a yakin baya bayan nan da kasar Amurka ta kaddamar a kanta , kuma Bagadaza a shirye take ta zurfafa yin aiki tare da Tehran , babu abinda ya kara karfafa dangantakar dake tsakaninsu shi ne daukar mataki a tsaron iyakoki da kulla yarjejeniyar hadin guiwa a fadin yankin.