Isra’ila Ta Sanar Da Kwace Cibiyar Bada Horo Ta UNRWA

a cigaba da taaddanci da isra;ila ke yi a yankin Gaza ta kwace wata cibiyar bada agaji a jiya.

Sojojin Isra’ila ta kwace cibiyar bada horo ta hukumar bada agaji ta majalisar dinkin duniya UNRWA a gabashin birnin Kudus, lamarin ya sanya hakulan sun karkata game da makomar hukumar dake gudanar da ayyukan jinkai a yankin falasdinu

sojojin Isra’ila sun kutsa kai a cibiyar bada horo ta kalandiya a jiya talata da safe kamar yadda kungiyar ta UNRWA ta sanar, tace akalla motoci guda 4 ne suka shiga cikin harabar cibiya tare da rakiyar akalla sojojin 50,lokacin da ma’aikatan UNRWA ke zaune acikin cibiyar, a hukumance sojojin Isra’ila sun sanar cewa gwamnatin sahyuniya ta kwace cibiyar

kungiyar bada agaji  ta UNRWA ta yi  tir da wannan mataki da isra’ila ta dauka kan wannan cibiya, tace shigar sojoji cikinta ba tare a izinin majalisar dinkin duniya ya sabama doka kuma ba zaa taba amince da shi ba, kuma ta ce cibiyar ta KTC tana daga cikin tsoffin wajen horas da matasa falasdinawa yan gudun hijira  yadda za su dogara da kansu .

kungiyar ta UNRWA ta yi kira ga kasashen duniya masu fada aji  da su dauki matakin gaggawa kuma da gaske don kare cibiyar ta UNRWA  dake kalandiya da sauran dukkan kayan aiki na majalisar dinkin duniya dake gabashin birnin Kudus da isra’ila ta mamaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted