Majalisar Ɗinkin Duniyar da Ƙungiyar agaji ta ICRC sun yi gargaɗi game da yadda duniya ke amfani da makamai masu sarrafa kansu wajen kashe ɗimbin fararen hula, inda suka yi kira na a ɗauki matakan gaggawa game da wannan matsala.
Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres da shugaban ƙungiyar agaji ta ICRC Mirjana Spoljaric ne suka gabatar da wannan gargaɗi a wata sanarwar haɗin gwuiwar da suka fitar.
Shugabannin biyu sun ce wuce makaɗi da rawa ne yadda ƙasashe ke shirin fara amfani da makaman da na’ura ke sarrafa su wajen kashe tarin mutane.
Shugabannin biyu sun buƙaci tattaunawa domin taƙaita amfani da irin waɗannan makamai, da suka ce ana gaba da fara aiki dasu a rikice-rikicen dake afkuwa a sassan duniya.
Hukumomin sun ce dole ne a fara tattaunawa nan take game da irin dokokin da za a gindaya wajen amfani da waɗannan makamai masu haɗarin gaske, don fito da haramcinsu da kuma ƙa’idojin amfani dasu ƙarara.