Rahotanni sun bayyana cewa kasahen Iran da Oman sun sanar cewa sun tattauna kan mataken da za’a bi wajen ganin zirga-zriga na gudana cikin tsari a mashigar Hurmuz, da kuma hanyar hadin guiwa ta jirgen ruwa ta wucin gadi.
Tattaunawar ta gudana ne yayin ziyarar aiki da ministan harkokin wajen kasar Oman sayyid Badr Albusaidi ya kawo nan birnin tehran inda ya tattauna da takwaransa na kasar iran sayyed Abbas Araqchi kamar yadda yake a jawabin hadin guiwa da suka fitar
Dukkan bangarorin biyu sun nuna cewa shawarwarin na su sun mayar da hankali ne kan sake dawo da zirga-zirgan ruwa cikin tsaro da aminci a mashigin tekun da kuma kare yanci kai da kuma yanci kasashen guda biyu
shawarwarin da aka bayar za’a fara bude hanyar ta wucin gadi a mashigar , kuma zaa ci gaba da tattauna ta kwararru kan yadda zaa samar da hanyar yin zirga zirga ta din din din da kuma kulla yarjejeniya kan yadda makomar gudanar da mashigar ruwa zai kasance a hukumance.