Shugaban cibiyar Al-Mustafa ta raya ilmin zamani tsakanin musulmi Dr Ali Akbar Salihi ya bayyana cewa kan iyakoki tsakanin musulmi a kasashen duniya daban daban ba zai hana cibiyar ta zami wani musulmi daga wasu kasashen duniya inda musulmi tsiraru ne ba don samun kyautar cibiyar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Dr Ali Akbar Salihi yana fadar haka wa taron yan jarida a dai dai ranar fara makon hadin kai tsakanin Musulmi a nan Tehran.
Salihi ya kara da cewa cibiyarsa tana iya zaben wani masani musulmi daga kasashen da ba musulmi ba don karban kyautar Al-Mustafa (s) wanda cibiyarsa take bayar wa a duk shekaru biyu-biyu.
Ya ce Kyautar Al-Mustafa zata kasance wani masomi ne na zaburar da musulmi a ko ina suke a duniya, wadanda suka taka rawa wajen ci gaba a harkar ci gaban ilmi a duniya. Yace manufar kyautar har iyala yau nita ce farfado da ci gaban addinin musulunci a wannan zamanin.
Cibiyar Musfada dai tana bada kyautar kudade ga wasu musulmi da suka zaba a cikin wadanda suka bukaci kyautar amma kuma suka yi ayyukan ci gaban ilmi a cikin musulmi a ranar maulidin manzon All..(s).
A yau ne ake fara makon hadin kai a nan kasar Iran wato daga 12-17 ga watan Rabi’il Awwal, makon da Imam Khomaini(q) ya bukaci hadin kai tsakanin musulmi shia da sunna don amfanin kansu a gaban makiyansu.