Qalibaf: Takunkuman Tattalin Arziki Kan Iran Yaudarar Ce

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran sannan shugaban tawagar tattaunawa da Amurka ya bayyana cewa kokarin Amurka na kara tsananta takunkuman tattalin arziki kan Iran, wani

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran sannan shugaban tawagar tattaunawa da Amurka ya bayyana cewa kokarin Amurka na kara tsananta takunkuman tattalin arziki kan Iran, wani shiri ne na hada Iran fada da kasashen duniya wanda Amurka ba zata iya ba.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Qalibasf yana fadar haka a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa, sanarwan da sakatarin baitul Malin Amurka Scott Besseny ya bayar a cikin yan kwanakin da suka gabata danghane da kara takurawa tattalin arzikin kasar Iran tare da tursasawa sauran kasashen duniya da kuma kamfanini masu zaman kansu taimaka mata kan hakan wani al-amari ne wand aba zai faru ba.

Ya ce a halin da ake ciki Amurka bata da karfin da zata tilastawa kasashen duniya maida kasar Iran saniyar ware, bata da karfin tattalin arzikin yin haka ko kuma karfin sojen tilasta masu yin hakan.

Qalibof ya kara da cewa, tuni kasashen da muke harkar kasuwnanin da su, sun fadawa duniya ta kafafen yada labarai, sun kuma aiko mana sako a rubuce kan cewa ba ruwansu da umurnin kasar Amurka dangane da kasar Iran.

Sakatare Bessent dai ya bayyana cewa Amurka zata hana Iran samon ko kondola daga waje kasar sai ta mikakai ga bukatun Amurka ko kuma gwamnatin ta rsuhe.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted