Kanada ta sanar da sanya haraji a kan sama da kayayyakin da ake kerawa a Amurka guda 700, ta tunkari masana’antu daban daban na amurka ne a matsayin mayar da martani kan sabbin harajin da gwamnatin trump ta kakaba mata
Ministan kudi na kasar kana Francios Philipe da kuma ministan masana’antu melenie joly ne suka sanar da sabon harajin a jiya talata kuma sun bayyana shi a matsayin martani kan abin da Ottawa ta ganin na rashin kyautatawa daga ma’aikatar kasuwanci ta Amurka,
Sabon harajin zai kunshi dukkan harajin na dalar kanada biliyan 27.6, kan kayayyakin da amurka take fitarwa da ya kunshi kashi 25% zuwa 50% da za su fara aiki a ranar 8 ga watan satumba, kuma harajin zai yi aiki ne akan kayayyakin da ake yinsu a kasar Amurka
Haka zalika ya kara da cewa harajin zai kunshi karafa, kayan madara kayayyakin noma, takardu da kayayyakin ado da shafe-shafe na mata da kuma kayayyakin katakai da sauran naurorin yin aikace –aikace. haka kuma kayan yan kasuwa da suka hada da naurar sanyaya wuri da sauransu zaa biya harajin kashi 15%
Wannan yana zuwa ne bayan tattaunawa da aka yi tsakanin Ottawa da Washington ba tare da cimma nasara ba, da ya sa shugaban Amurka Donald trump ya kakabawa kasar kanada sabon haraji akan kayayyakinta.