Kasar China ta nuna kin amincewarta da takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran, tana mai kara da cewa za ta kare hakkinta da kuma manufofin kanfanoninta.
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto kakakin ofishin jakadancin China dake Amurka Leo T Chang yana fadin haka a yayin da yake mayar da martani akan sanarwar da Amurkan ta fitar na jerin kafanonin Iran da ta kakaba wa takunkumi.
Jami’in diplomasiyyar ta kasar China yana cewa takunkumin na Amurka ya sabawa doka, kuma ba shi da wata madogara ta dokokin kasa da kasa, sannan kuma kwamitin tsaro bai da hannu a cikinsa.
Takunkumin na Amurka akan Iran dai ya biyo bayan gajiyawarta ne a fagen yaki, da ta kasa cimma dukkanin manufofin da ta Shata akan Iran.
Mahukuntan Iran sun bayyana cewa za su yi aiki domin dakile manufofin takunkuman da hana su cimma manufar Amurka, kamar yadda a fagen daga ta kasa cimma komai.