Iran Ta Isar Da Sharuddan Bude Hurmuz Ga Pakistan

Gwamnatin kasar Iran ta mikawa feil Mashak Asim Munir babban kwamandan sojojin kasar Pakistan sharuddan kasar na bude mashigar ruwa ta Hurmus, daga ciki har

Gwamnatin kasar Iran ta mikawa feil Mashak Asim Munir babban kwamandan sojojin kasar Pakistan sharuddan kasar na bude mashigar ruwa ta Hurmus, daga ciki har da komawa kan yarjeniyar Islamabad.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto wata majiya kusa da tawagar tattaunawa da Amurka bayan yakin baya bayan nan tana cewa, sabanin yanda wasu suka bayyana dalilan ziyarar da Munir ya kawo nan Tehran a jiya Litini, baya dauke da wani sako daga Amurka, sai dai ya zo Tehran ne don bibiyar inda aka kwana dangane da tattaunawa tsakanin kasashen biyu, da kuma karban duk wani sakon da ake da shi zuwa Amurkawa.

A lokacin tattaunawa da Mr Munir tawagar ta fayyace matsayin kasar dangane da mashigar ta Hurmusz, sannan Iran bata sauya matsayinta ba. Dole ne kamar yanda majiyar ta bayyana, Amurka ta dawo kan takardan fahintar Juna da ita, ta kuma aiwatar da dukkan bukatun Iran da suke cikinta, daga ciki har da bukata ta 5, ta amincewa da ikon kasar Iran a kan wannan mashigar har’abada. .

Daga karshe majiyar ta kammala da cewa, Iran ta bukaci Munir ya isar da wannan sakon ga Amurkawa kamar yanda yake.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted