Shugaba Bola ahmed Tinubu na tarayyar Najeriya ya yi kira ga musulman kasar su koikoyi annabi Muhammadu (a) a halayensa, su kuma yiwa kasar addu’a.
Jaridar Daily Trunst ta Najeriya ta nakalto shugaban yana taya al-ummar musulmi na kasar murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halittu, a sakonsa na Maulidin manzon All..(s) a yau Talata. Ya kuma kara da cewa muminai su yi amfani da wannan damar don addu’a da kuma neman All..ya daukewa kasar mummunan halin da take ciki, na rashin tsaro a duk fadin kasar.
Bayo Onanuga mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin watsa labarai wanda kuma ya sanya hannu a takardan sakon shugaban kasar, ya ce : Shugaba Tinubu ya bukaci muminai su yi biyayya ga karantarwar annabi Muhammadu (s), yace akwai darussa masu yawa wadanda zamu dauka a karantarwarsa, wadanda suka hada da juriya, mutunci, rashin son kai da kuma hakuri.
Daga karshe shugaban ya bukaci malaman addini su yi amfani da wannan lokacin don yin addu’a wa kasar, da kuma kira zuwa ga mabiyansu su maida karantarwa manzon All..(s) abin koyi a aikace a tsakaninsu.