Xin Hua: Tasirin Takunkuman Amurka Akan Iran Zai Shafi Tattalin Arzikin Duniya

Kamfanin dillacin labarum China Xin Hua ya jaddada cewa; Matsin lambar tattalin arziki na Amurka akan Iran, ba wai Amurkan ce kadai ita ma zai

matsayar China Akan Takunkumin Iran

Kamfanin dillacin labarum China Xin Hua ya jaddada cewa; Matsin lambar tattalin arziki na Amurka akan Iran, ba wai Amurkan ce kadai ita ma zai shafa ba, zai kuma shafi tattalin arziki kasashe da dama a duniya.

Rahoton musamman na kamfanin dillancin labarun China ya kuma ce; Abinda Amurkan take son ganin ya faru shi ne ta yi matsin lamba na tattalin arziki akan Iran da hakan zai kai ga Iran ta mika mata wuya.

Sai dai kuma tarihi ya nuna cewa, yakin tattalin arziki da siyasar matsin lamba ta koli ba su ne hanyar warware matsaloli irin wanann ba, kamar yadda rahoton ya nuna. Haka nan kuma ya ce, yau da gobe ta tabbar da cewa matsin lambar tattalin arziki irin wannan tana kara hatsari da bullar matsaloli ne.

A jiya ne dai ministan harkokin wajen kasar China Lin Jian ya bayyana rashin amincewar kasarsa da wannan takunkumin, sannan ya kara da cewa; Alakar kasashen biyu ta ginu ne akan dokokin kasa da kasa, kuma kasarsa za ta kare hakkoki da manufofinta da suke halartattu wajen fuskantar matakan  na Amurka.

 Haka nan kuma ministan harkokin wajen kasar ta China ya ce; Ba zai yiyu a yi aiki da takunkumai akan kasashen da suke mu’amala ta kasuwanci da Iran ba.

Shi ma kakakin ma’aikatar harkokin wajen China ya fada a ranar Litinin cewa aiki da wannan takunkumin babu abinda zai haifar sai karuwar rikici, kuma ba zai amfani kowane bangare ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted