Iran Ta Karyata Jita-Jitar Da Kasar Sweden Ta Yada Na Korar Jami’inta

kasar iran ta karye zargin bada waadin sa'oi 48 ga jamiin diplomasiyar Sewede ya fice daga iran

Rahotanni sun bayyana cewa kasar iran ta musanta jita-jitar da kasar Sweden ta ke yadawa na cewa kasar iran ta bawa jami’in diplomasiyarta saoi 48 da ya bar birnin Tehran, a matsayin martani ga matakin da Stockholm ta dauka na hana wani jami’in diplimasiyar Iran ci gaba da gudanar da ayyukansa a kasar Sweden

A cikin bayani  da ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta fitar a yau Alhamis tayi tir da matakin da kasar Sweden ta dauka na hana wani jami’in diplomasiyar iran a ofishin jakadancinta dake Stockhum ci gaba da ayyukansa, yace zargin da aka yi wa iran bashi da tushe ko kadan

Yace matakin da kasar Sweden ta dauka babu adalci a ciki kuma yayi hannun riga da dokokin kasa da kasa na tilastawa wani jami’in diplomasiyar iran dake aiki a ofishin jakadancinta da ya bar kasar Sweden ba tare da wani kwakkwaran dalili ba,

Kuma a lokaci guda gwamnatin kasar Sweden tana  zargi mara tushe na  hannun irin kan batutuwan da suka shafi tsaro a kasar ta, kuma tuni ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta yi watsi da wannan zargi kuma ta bayyana matakin na Sweden kan jaimi’in diplomasiyar iran a matsayin rashin adalci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted