Marine Le Pen: Iran Tana Karfi Fiye Da Yadda Trump Ya Zata

Shugabar jam’iyyar masu ra’ayin mazan jiya ta Faransa Marine Le Pen ta bayyana cewa; Iran kasa ce mai sarkakiya wacce kuma take da karfi fiye
hoton Le Pen

Shugabar jam’iyyar  masu ra’ayin mazan jiya ta Faransa Marine Le Pen ta bayyana cewa; Iran kasa ce mai sarkakiya wacce kuma take da karfi fiye da yadda shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zata.

Marine Le Pen wacce talbijin din kamfanin dillancin Labarun Reuters tana magana akan harin wuce gona da iri na Amurka da Isra’ila akan Iran, sanann ta yi magana akan Trump tana cewa: “ Ya kamata mu fahimci yanzu me yake son yi a can, domin har yanzu ba mu fahimci manufarsa ba.”

Haka nan kuma ta kara da cewa: Trump bai cimma manufofinsa na yaki akan Iran ba, ga shi kuma duniya duniya cikin hatsarin hauhawar farashi wanda yana da nashi illolin ga duniya baki daya.

Har ila yau Marine Le Pen ta ce; Ya kamata a nai wa Amurka shawarar ta daina shiga yaki da kasa mai tsawon tarihi, kuma daula mai sarkakiya,wacce kuma a Zahiri tana da karfi fiye da yadda Donald Trump ya dauka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted