Yemen: Shugaban Ansarullah Ya Kore Labarin Da Saudiyya Ta Watsa Na Cewa Sun  Nufi Birnin Makka Mai Alfarma Da Hari

Yemen: Shugaban Ansarullah Ya Kore Labarin Da Saudiyya Ta Watsa Na Cewa Sun Nufi Birnin Makka Mai Alfarma Da Hari
Husy

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husy ya kore labarin da Saudiyya ta watsa na cewa sun kai wa birnin Makka mai alfarma hari, tare da bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na rufe kashin da suke sha a Yemen.

Sayyid Abdulmalik al-Husy wanda ya gabatar da jawabi a jiya Alhamsi, ya ce; Saudiyya a karkashin kawancenta na yaki da Yemen ta rusa da lalata fiye da masalaltai 2000 da kuma cibiyoyin addini.

Sayyid Abdulmalik al Husy ta kuma ce; Batun kai wa Makkah hari, karya ce babba, tare da jaddada cewa;al’ummar Yemen mutane ne masu Imani, babu yadda za su kai hari akan wurare masu tsarki na addini ko su amince da a kai musu hari.”

Sayyid Abdulmalik al-Husy ya kuma ce; Mutanen Yemen a shirye suke su saudaukar da kawunansu da dukiyarsu domin kare Makka mai alfarma.

A jiya Alhamis ma dai an yi taron malaman addinin musulunci a birnin Sanaa inda aka yi tir da wannan sabon makircin na Saudiyya wanda ya shigar da batun Makka mai tsarki a cikin siyasa da kokarin samun goyon bayan musulmin duniya bayan da su ka sha kashi a hannun sojojin Yemen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted