DRC: Likitoci Suna Cikin Mawuyacin Yanayi A Kokarin Magance Cutar Ebola

Ma'aikatan kiwon lafiya na kasar DRC suna fuskantar matsanancin yanayi a kokarin da suke yin a magance cutar Ebola da ta barke a cikin kasar.
kokarin hana yaduwar Ebola

Ma’aikatan kiwon lafiya na kasar DRC suna fuskantar matsanancin yanayi a kokarin da suke yin a magance cutar Ebola da ta barke a cikin kasar.

Ya zuwa yanzu an tabbatar da cewa mutane fiye da 7,000 ne su ka kamu da cutar tun barkewara a cikin watan Mayu na wannan shekara. Haka nan kuma mahukuntan kasar sun sanar da cewa an sami mutuwar wasu mutane da sun kai 3,000.

Shugaban cibiyar kiwon lafiya mai aiki da kungiyar “Likitoci Ba Tare Da Iyaka Ba.” Fabrice Ngoyi Nsakalumpu ya fada wa manema labaru cewa;

“Ba abu ne mai sauki ba, yin aiki a kasa ta, ya zamana kana ganin yadda al’umma su ka kamu da cutar Ebola, sannan ya zamana babu wani tsayayyen magani, kuma ya zamana marasa lafiyar suna fuskantar wahala kafin su isa cibiyoyin kiwon lafiya.”

Gabashin kasar ta DRC ne dai cibiyar bullar wannan cuta wacce kuma a lokaci daya  yake fama da tashe-tashen hankula. Har ila yau wadanda su ka kamu da wannan cutar suna fuskantar tsangwama daga al’umma.

Ya zuwa yanzu wannan cutar ta bulla a cikin wasu yankun da sassa na kasar ta DRC. Mahukunta suna cewa da alama cutar ta kai koli bayan da a halin yanzu ta fara ja da baya.

A kasar Uganda mai makwabtaka da DRC an sami mutane 20 da su ka kamu da ita, daga cikinsu da akwai mutane 2 da su ka rasa rayukansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted