Kotun Isra’ila Ta Tsawaita Ci Gaba Da Tsare Yar Rahoton Press TV

wata kotu a Isra'ila ta yanke hukumci cigaba da tsare yar rahoton press tv

wata kutu a haramtacciyar kasar Isra’ila ta tsawaita lokacin ci gaba da tsare yar rahoton kidan talabijin din press Tv na kasar Iran Naqaa Hamed har zuwa 23 ga watan satumba da muke ciki, a ci gaba da kokarin da isra’ila ke yin a rufe bakin yan jarida masu yanci a yammacin kogin Jodan da ta mamaye

Ita dai Hamed yar shekaru 38 ne da haihuwa kuma sojojin Isra’ila sun kama ta ne a ranar 14 ga watan satumba a wani wajen binciken ababen hawa dake kusa da Tuqu a baithlaham.inda suka raba ta da mai dauka mata kamara, kuma aka wuce da ita zuwa wani wuri da baa sani ba,

Bafalasdiniya kuma mai takadar shedar zama baamurkiya kuma mahaifiyar yara 3 Hamed ta kwashe shekaru 15 tana bada rahotanni kan abubuwan da suka shafi siyasa da kuma wadanda suka shafi rikice-rikice.

kamun nata yazo ne bayan an dade ana kai mata hare hare na zahiri da kuma na yakin kwakwalwa, a watan Decemba na shekara ta 2025 da kuma watan Agustan shekara ta 2026 sojojin isra’ila sun ji mata rauni da gangan inda suka harbeta da harshin roba, da kuma buga mata hayaki mai sa hawaye duk da yake cewa ta sanya da kayan da ke nuna cewa ita yar jarida ce a sansanin yan gudun hijira na Qalandiya

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted