Wakilin jamhuriyar musulunci ta Iran a MDD ya yi jinjina da yabo ga kasashen Rasha da Amurka saboda hawa kujerar naki da su ka yi akan daftarin kudurin da Amurka ta gabatar da shi akan Iran,haka nan kasashen Pakistan da Somaliya da su ka kada kuri’ar kin amincewa.
A jiya Alhamis ne dai ofishin wakilcin Iran a MDD ya fitar da bayani da a ciki ya bayyana cewa; A zaman da aka yi a yau Alhamis a kwamitin tsaro na MDD, Amurka ta gabatar da daftarin kuduri wanda manufarsa siyasa ce da zummar farafado da wani kwamiti da aka bai wa sunan na kwararru wanda ba ya bisa doka, amma kuma kudirin bai sami karbuwa ba.
Ofishin wakilcin na Iran ya kara da cewa kasashen Rasha da China sun sake kare dokokin MDD da dokokin kasa da kasa, su ka hana Amurka da kawayenta yin gaban kansu ta hanyar fakewa da kwamtin tsaro da hana su cimma manufofinsu na siyasa.
Ofishin wakilcin na Iran ya kuma ce; Iran tana yin jinjina da girmamawa ga Rasha da China saboda matakin da su ka dauka, haka nan kuma yin jinjina ga kasashen Pakistan da Somaliya akan matakin da su ma su ka dauka.
A yayin zaman kwamitin na MDD mai wakilai 15 kasashen Rasha da China sun kada kuri’un kin amincewa da daftarin kudurin da Amurkan ta bijiro da shi, sai kasashen Somaliya da Pakistan da su ka kaucewa kada kuri’a, yayin da sauran kasashe 11 su ka amince da shi.
Ana da bukatar kuri’y 9 domin amincewa da kowane daftarin kuduri a kwamitin tsaro, idan har babu wata daga cikin kasashe biyar masu tabbatattun kujeru da su ka hau kujerar naki.