Dakarun kare juyin musulunci na kasar iran a karo na 53 sun kakkabo jirgin sama mara matuki na Amurka kirar MQ-9 tun bayan da Amurka da isra’ila suka fara kai mata hari, na farkon su shi ne wani jirgin amurka wanda dakarun iran suka karboshi a lokacin yaki.
Dakarun kula da sararin samaniya na rundunar kare juyin musulunci na iran sun kakkabo wani jirgin yaki mara matuki na kasar Amurka da safiyar yau asararin samaniyar tsibirin Qeshm, inda suka yi amfani da sabon tsarin makamin kariya na sararin samaniya da ake juyashi daga nesa.
Da yake Magana a wajen taron da aka gudanar a yau alhamis brigadier janara Majid Ebn Redha mukaddashin ministan tsaro na kasa yace yakin baya bayan nan ya nuna irin balubalen da sojojin Amurka ke fuskanta wajen tunkarar makamai masu linzami da karfin ikon jiragen sama marasa matuki na kasar iran
Yace har ya zuwa jiya sojojin Amurka masu zalunci da ta’adanci sun dogara sosai akan makamansu da karfin sojinsu bisa laakari da ikirarin trumph mara tushe balle madafa