Ansarullah Ta karyata Ikirarin Saudiya Na Kai Hari A Makka

kungiyar ansarullah ta yamen ta karyata zargin saudiya na cewa yamen ta kai hari a makka
Husy

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yamen abdulmalik al-huthi yayi tir da zarge-zargen da kasar saudiya ke yadawa na cewa dakarun sojin kasar Yamen sun kai hari kan gari mai tsarki na makka, kuma yayi watsi da zargin, yace karyace kawai da kokarin rufe hare haren da take kaiwa kan fararen hula a kasar yamen

A cikin wani bayani da yayi a gidan talabijin din kasa a yau alhamis  Abdulmalik yace da gangan ne gwamnatin saudiya take ci gaba da yada karya don neman goyon bayan duniya su yi tir da wannan mataki, kuma sun yada zargin karya don rufe irin mummuna laifukan yaki da take yi kan fararen hula a kasar Yamen .

Ya ce babu wani musulmin kirki mai hankali dake darajta asalinsa na musulunci da zai yarda ko ya amincewa da irin wannan kazafin kan mutanen da Annabi mohammad mai tsira da aminci su tabbata gareshi da alayensa yayi shaida akan su  a matsayin mutane Imani da hikima

Daga karshe ya jaddada cewa mutanen Yamen suna tsananin girmama wurare masu tsarki na musulunci a ko ina duniya, kuma zargin da kasar saudiya ke musu cin zarafi ne kai tsaye ga alummar musulmin yamen da kuma mutucinsu

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted