MDD Ta Bai Wa Shugaban Falasdinawa Damar Yin Jawabi Daga Nesa Ta Hanyar Bidiyo

Matakin na MDD dai ya biyo bayan da Amurka ta hana shugaban na Falasdinawa Mahmud Abbas Abu Mazin Izinin shiga cikin kasar domin halartar taron

Matakin na MDD dai ya biyo bayan  da Amurka ta hana shugaban na Falasdinawa Mahmud Abbas Abu Mazin Izinin shiga cikin kasar domin halartar taron babban zauren MDD na shekara-shekara.

Jami’an gwamnatin kwarya-kwaryar Falasdinawa ta shaida wa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa; Amurkan ta hana musu izinin shiga kasar domin halartar taron babban zauren MDD da za a yi a mako mai zuwa.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da cewa za ta tsawaita takunkumin hana shiga cikin Kasar da ta kakaba wa jami’an Falasdinawa saboda sun  shigar da rikicinsu da Isra’ila,a fagen duniya.

A yau Juma’a ne dai za kada kuri’a a babban zauren MDD mai mambobi 193 da zai bai wa Mahmud Abbas damar gabatar da jawabi daga nesa a yayin taron da za a yi a mako mai zuwa.  A Watan Yuli na wannan shekarar Mahmud Abbas ya gabatar da jawabi ta Bidiyo daga nesa.

Ma’aikatar harkokin wajen Falasdinawa ta bayyana matakin na Amurka da cewa yana cin karo da kokarin da ake yi na sake karfafa a tsakaninsu da Amurka da kuma samar da yanayin da zai kai ga kafa Daular Falasdinawa da tabbatar da tsaro da zaman lafiya a cikin yankin gabas ta tsakiya.

A karkashin yarjejeniyar MDD ta 1947, wajibi ne ga Amurka ta bayar da viza ga jami’an diplomasiyya na waje domin halartar tarukan MDD. Sai dai Amurka ta ce za ta iya kin bayar da izinin shiga bisa dalilai na tsaro da tsattsauran ra’ayi da kuma wasu dalilai na siyasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted