Ƙungiyar Kwadago ta NLC a Najeriya ta bukaci gwamnatin kasar ta samar da wani kunshin rage radadi ga ma’aikata a ilahirin sassan kasar sakamakon yadda sake kara farashin man fetur ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki.
Har ila yau NLC ta bukaci gwamnatin Najeriyar ta gabatar da wasu tsare-tsare da zasu taimaka wajen rage yawaitar hauhawar farashin na man fetur, tare da tabbatar da ganin ana sayar da danyen man ga matatun cikin gida a takardar kudi ta naira maimakon dala.
A cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun shugabanta na kasa, Joe Ajaero ta ce wajibi ne gwamnatin ta daukin matakin rage radadin da tsadar man ke haifarwa ga al’ummar kasar musamman ma’aikata. A manyan biranen Najeriyar ana sayar da kowacce lita ta man fetur kan farashin naira dubu 1 da 430 a wani yanayi da bayanai ke cewa a wasu yankunan farashin ya haura haka, batun da NLC ke cewa tashin farashin man zai sake tsawwala rayuwa ga jama’ar kasar.