Search
Close this search box.

WFP: Idan Ba A Shigar Da Abinci Cikin Gaza Ba Dubban Yara Za Su Mutu

Hukumar Abinci ta duniya  ( WFP) wacce take karkashin MDD, ta sanar da cewa, matukar ba a bari aka shigar da kayan abinci cikin Gaza

Hukumar Abinci ta duniya  ( WFP) wacce take karkashin MDD, ta sanar da cewa, matukar ba a bari aka shigar da kayan abinci cikin Gaza ba, to makomar dubban kananan yaran yankin shi ne mutuwa,musamman ma dai a arewacin Gaza.

Wani babban jami’i a hukumar abincin ta duniya, Arif Hussain ya bayyana cewa; A halin yanzu da akwai kananan yaran da suke mutuwa saboda yunwa,kuma muna gab da shelanta bullar yunwa a hukumance a wannan yankin na Arewacin Gaza.

Arif Hussain wanda ya gabatar da taron manema labaru ta hanyar bidiyo daga nesa, ya bayyana cewa; Shelanta bullar yunwa a hukumance a Gaza, yana nufin mun ci kasa, kuma mutane da su ka hada da kananan yara sun mutu.

Jami’in hukumar abincin ta duniya ya yi kira da a dauki matakin gaggawa domin hana fadadar yunwa, idan kuwa ba mu shigar da abincin ba, to dubban yara ne za su mutu.

Tun da HKI ta shelanta yaki akan Gaza ne, ta sanar da cewa za ta killace yankin ta hana a shigar da kayan abinci da magani da ruwan sha, bayan da ministan yakin HKI ya  bayyana Falasdinawa da dabbobi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments