Hukumar Abinci ta duniya ta fitar da wani rahoto akan halin da ake ciki dangane da ayyukan jin kai a kasar Sudan ta kudu da aciki ta bayyana cewa; Da akwai mutum miliyan daya da suke fuskantar rasa abincin taimako a wannan kasa.
Rahoton ya yi Ishara da rikice-rikicen da ake fama da su a cikin kasar Sudan mai makwabtaka da ita, da zai jefa mutane miliyan daya cikin matsalar rashin abinci.
Hukumar wacce take a karkashin Majalisar Dinkin Duniya ta kuma kara cewa; A halin yanzu da akwai mutane miliyan 7.8 wadanda suke gogoriyin neman abinda za su ci a kowace rana. Haka nan kuma da akwai wasu kananan yara miliyan 2.2 da mata masu ciki miliyan 1.2 da masu shayar da yara da suke da bukatuwa da agajin gaggawa.
Mataimakin babban daraktan zartarwa na hukumar Abincin na duniya ( WFP) Matthew Hollingworth ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labaru a birnin Geneva.
Haka nan kuma ya ce matukar ba a samu Karin taimako ba, to wasu mutane da za su kai miliyan daya za su rasa samun abincin da za su ci domin sur ayu daga nan zuwa watan Oktoba.
Hukumar ta ce a halin yanzu tana da gibin kudin da sun kai Dala miliyan 86,idan kuwa aka isa watanni shida masu zuwa, to za a bukaci abinda zai kai dala miliyan 400. A kasar Sudan ma dai hukumar abincin ta bayyana yadda ci gaba da yaki yake ci gaba da jefa rayuwar al’ummar kasar cikin wahala da ci gaba da fuskantar rashin abinci.