Gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa batun sake gina zirin gaza a halin da ake ciki bata taso ba, saboda masu rusawar suna nan, matukar HKI ta ci gaba da kasancewa a yankin yammacin Asia sake gina gaza bai da wani amfani, don zasu sake rusa shi.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Sadeq Qorbani jakadan JMI a Geneva da kuma sauran cibiyoyin MDD a kasashen Turai yana fadar haka a taro Kasuwanci da ci gaba UNCTAD
karo na 73 a Geneva. Ya kuma kara da cewa ba zai yu a yi maganar sake gina gaza al-ahali mai rusa ta yana nan bai gushe ba. Don haka dole ne HKI ta kau daga yankin yammacin Asiya kafin a yi maganar sake gina Gaza.
Ya ce a halin yanzu HKI ta rusa kasha 92% na tattalin arzikin gaza kuma mizanin ci gaba a yankin ko GDP bai fi 212 a shekara ta 2025 ba. Ana bukatar akalla dalar Amurka billion 71.5 a farko wannan shekara don sake gina yankin. Kuma hakan zai dauki shekaru.