Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov ya ce; ko kadan Moscow ba ta da niyyar kai wa kasashen turai hari, amma kuma tana gargadin idan har turawan su ka kai wa Rasha hari, to yakin ba zai dauki lokaci mai tsawo ba.
Ministan harkokin wajen na Rasha wanda yake Magana a yau Laraba a birnin Moscow ya ce; Mun sha jaddada cewa ba mu da niyyar kai wa turai hari, amma kuma kowace rana kasashen na turai su na yin Magana akan yaki da Rasha, da kai wa Rasha hari, to idan hakan ta faru, yakin ba zai dade ba za a kare shi.”
Ministan harkokin wajen na Rasha ya kuma zargi kasashen turai din da amfani da kowace kazamar hanya domin kare manufofinsu.