Araqchi: Iran Zata Bayyana Irin Hasarar Da Ta Janyowa Amurka

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran ya bayyana cewa: Za su bayyana irin hasarar da Amurka ta yi a yakinta da Iran nan gaba Ministan Harkokin

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran ya bayyana cewa: Za su bayyana irin hasarar da Amurka ta yi a yakinta da Iran nan gaba

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Abbas Araqchi ya mayar da martani ga ikirarin jami’an Amurka, yana mai ikirarin cewa ba su da tushe kuma yana ambato daga majiyoyin Amurka.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Mehr, a martanin da ya mayar kan ikirarin da jami’an Amurka suka yi cewa: Iran ba ta da kariya, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya rubuta a dandalin X cewa: Ikrari Amurka cewa Iran ba ta da kariya da’awa ce kawai maras tushe da madogara.

Araqchi ya jaddada cewa: A gaskiyar zance Iran ta samu nasarar lalata daruruwan sansanonin sojin Amurka da wuraren aiki, kuma kona jiragen saman Amurka da dama.

Ya kuma jaddada cewa: Za su bayyana ainihin adadin hasarar da Amurka ta yi a yakinta da Iran nan gaba.

Kunya za ta ci gaba da kasancewa ga waɗanda suka yi iƙirarin karya cewa: Iran ba ta da kariya!

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted