IRGC: Amurka Ta Kirkiro Kissar Matukin F-15 Da Aka Kakkabo A Iran

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci a nan Iran wato IRGC sun bayyana cewa kisser kakkabo jirgin yakin Amurka samfurin F 15 a cikin kasar

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci a nan Iran wato IRGC sun bayyana cewa kisser kakkabo jirgin yakin Amurka samfurin F 15 a cikin kasar Irana farkon yakin da Amurka da HKI suka dorawa JMI, wanda tashar talabijan ta CBS ta watsa ya yi kama da shirin majigin Holywood ne.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto kakakin rundunar Burgedia Janar Hossain Muhebbi kakakin rundunar yana fadar. Ya kuma kara da cewa hoton mutumin da tashar CBS ta watsa a matsayin matukin jirgin na F 15 da kuma kisser da ya bayar bai yi kama da gaskiya ba.

Musamman inda yake magana kan cewa yana gudun kilomita 160 a lokacinda garkuwan samaniyar kasar Iran suka kakkabo jirginsa, da kuma inda yake cewa leman cetonsa ya ki budewa don haka ya fadi a kan tsaunuka  a yankin da kuma ji raunuka da dama.

Janar Muhibbi ya bayyana cewa, Amurka tana cikin damuwa soai dangane da asarorin da tay yi yakin da take ci gaba da fafatawa da JMI. Don haka zata yi duk abinda zata iya yi musamman a lukatan zabe don wanke fuskanta daga abinda kunyan da ya faru a yakin.

Janar Muhammbi ya ce babu wani mai hankali da zai amince kissar kakkabo jirjin yakin Amurka samfurin F 15 a cikin watan Afrilun da ya gabata a nan kasar Iran.

Ya kuma  kammala da cewa wannan wasan koikoyon da suka shirya ba zai wanke Amurka da abin kunyar da ta fuskanta a yakinta da JMI ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted