Iran: Yakamata Duniya Ta Sa Ido Kan Afghanistan

Jakadan JMI a MDD a birnin New York, ya bayyana cewa Tehran tana sanna ido akan al-amura a kasar Afghanistan, kuma ya zuwa yanzu tun

Jakadan JMI a MDD a birnin New York, ya bayyana cewa Tehran tana sanna ido akan al-amura a kasar Afghanistan, kuma ya zuwa yanzu tun zuwan sabuwar gwamnatin kasar shekaru kimani 5 da suka gabata, an sami raguwar tashe tashen hankula a kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Gholamhussain Darzi yana fadar haka a taron kwamitin tsaro na MDD dangane da kasar Afghanistan. Darzi ya ce, amma har yanzun akwai kungiyar ISIS-Khurasan har yanzu a kasar Afghanistan kuma su barazane ce ga kasashen yankin.

 Duk da cewa sun dade ba’a ji doriyarsu ba, amma suna nan kuma har yanzun su  barazana ne ga tsaron kasashen yankin. Don haka ya kara jaddada bukatar kasashen duniya su sanya ido a kan abubuwan da suka faru a kasar ta Afghanistan.

A jawabinda a gaban kwamitin tsaron Darzi ya kara da cewa kungiyar ISIL-K da wasu kananan kungiyoyin yan ta’adda suna nan cikin kasar ta Afghanistan, sai dai da alamun tsaron gwamnatin Afghanistan na wanan lokacin yana da karfi. Don haka muna iya cewa harkokin tsaro a kasar ya samu ci gaba sosai idan an kwatanta da lokutan baya.

Darzi ya kara da cewa, wani abu mai muhimmnaci da ya auku a kasar Afghanistan a shekarun da suka gabata shi ne raguwar noman Opium a kasar, wanda yake da matukar muhimmanci da lafiyan kasashen duniya musamman kasashe makobta.

Yakuma kammala da cewa har yanzun kasar Afghanistan tana bukatar kayakin agaji daga kungiyoyin kasa da kasa masu kula da yan gudun hijira da kuma na jinkai a cikin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted