Dakarun rundunar Kassam ta kungiyar Hamas sun sanar da shahadar daya daga cikin kwamandojinsu na yankin Rafah Atiyyah Muhammad Abu Ubaid wanda ake yi wa lakabi da “Abu Atiyyah”.
Abu Atiyyah ya yi shahada ne a jita Talata sanadiyyar kisan gillar da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi masa a jiya Talata.
Sanarwar ta Kassam ta ce; Abu Atiyyah ya yi shahada ne bayan lokaci mai tsawo na jihadi da sadaukarwa, domin ya fara aiki da rundunar Kassam ne tun a 1993, kuma ya shiga cikin farmaki daban-daban akan abokan gaba.
Daga cikin farmakin da Abu Atiyyah ta yi tarayya a cikinsu da akwai; Na hasumiyar “Hardun, da ” ta Ramukan Karkashin Kasa” da wasu da dama.
A lokacin da sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kai wa sansanin ‘yan hijirar Falasdianwa hari, a 2002, Abu Atiyyah” ne ya jagoranci mayakan Falasdinawa da su ka kare sansanin Rafah.
Har ila yau, Kassam ta bayyana shahidin da cewa yana daya daga cikin kwamandojin farmakin ” Guguwar Aqsa” na 2023 wanda ya rikita wa ‘yan sahayoniya lissafi. Bayan shahadar Muhammad Shaabana ne a matsayin kwamandar rudnunar Rafah, Abu Atiyyah ya maye gurbinsa.
Kassam ta sha alwashin ci gaba da tafiya akan godaben shahidin na jihadi da gwgawarmaya da dorawa daga inda ya tsaya.
A jiya Talata ne dai sojojin Sahayoniya su ka kai hari akan yankin al-baidar dake kudu masu yammacin birnin Gaza. Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun ce sun kashe Shahidin ne a wani farmaki na hadin gwiwa da kungiyar leken asiri ta “Shabak”