Wall Street:  Yakin Iran Ya Sa Amurkawa Sun Kashe Karin Kudi Dala Biliyan  100 Na Sayen Makamashi

Jaridar "Wall Street Journal ta buga labarin da yake cewa; Tashin farashin man fetur sama da dala 100 kowace ganga ya jefa Amurka cikin wani
famfon mai

Jaridar “Wall Street Journal ta buga labarin da yake cewa; Tashin farashin man fetur sama da dala 100 kowace ganga ya jefa Amurka cikin wani yanayi mawuyaci da ya sa mutanen kasar su ka kashe Karin kudin da sun kai Dala biliyan 107.

Jaridar ta ce ba domin yakin ba to da Amurkawan ba su kashe wadannan kudaden ba wajen sayen fetur da Desel ,haka nan shi ma yakin Rasha da Ukrain ya taka rawa wajen karuwar farashin.

Haka nan kuma jaridar ta ce tun daga fara yakin Amurka da Isra’ila akan Iran a ranar 28 ga watan Ogusta, a kowace rana Amurkawa suka kashe Karin kudin da sun kai dala miliyan 500.

Bugu da kari, jaridar ta yi hashashen cewa anan gaba za a iya samun karuwar farashin.

Tashin farashin makamashin zai kuma shafi yadda Amurkawan za su kashe kudin makmarantar yaransu a shekarar bana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted