Saudia Tana Fama Da Karancin Garkuwan Makamai Masu Linzami

Gwamnatin kasar Saudia tana fama da tsananin karancin garkuwan makamai masu linzami don kakkabo makamai masu linzamisamfurin Bilistic a dai lokacinda yaki yana kara tsanani

Gwamnatin kasar Saudia tana fama da tsananin karancin garkuwan makamai masu linzami don kakkabo makamai masu linzamisamfurin Bilistic a dai lokacinda yaki yana kara tsanani tsakanin da da gwamnatin kasar Yemen ko kuma kungiyar Ansarallah.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Associated Press na fadar haka. Ya kuma kara da cewa tuni gwamnatin bin Salman ta mika hannun roko ga kasashen Turai don samun wasu daga cikin makaman kariya ko garkuwa da makamai masu linzami da kuma Drone na dakarun Ansarallah.

Masaa Press ta kasar Yemen ta nakalto Associated Press a cikin tattaunawa da Jami’an kasar Saudia, na cewa sun yi magana da kasashen Burtania Faransa Pakistan da kuma Masar don samun wasu daga cikin makamai kuma garkuwa daga makamai masu linzami na Ansarallah.

Labarin ya kara da cewa Saudia ta koma zuwa ga wadan nan kasashe ne saboda garkuwan makamai masu Linzami da Drones nakasar Amurka sun kare a cikin fafatawarta da kasar Iran a cikin watanni 6 dasuka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted