Iran Ta Yi Watsi Da Jamus Dangane Da Yakin A Iran

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Bakaei, ya yi watsi da zancen magajin garin kasar Jamus dangane da yaki a Iran da shirinta na

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Bakaei, ya yi watsi da zancen magajin garin kasar Jamus dangane da yaki a Iran da shirinta na makamashin Nukliya da abinda ya kira wakilanta a kasashen yammacin Asia da dsauransu.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Isma’il Bakhaei yan fadar haka a shafinsa na X a jiya laraba. Ya kuma kara da cewa, shugaban kasar ta Jamus ya manta da wadanda suka fara yakin gaba daya a maganarsa, wadanda kuma kawayen Jamus ne wato Amurka da HKI.

Ya ce, bai kawo abinda ya haddasa yakin ba, sai dai yana maganar wakilan iran a yankin, wadanda a wajemmu inji shi, kungiyoyi ne masu neman yancin kansu da kuma hakkokinsu da aka kwace, Ya ce, Cancalon Jamus yana kungiyar Hizbullah ta mika kai ga HKI ta mamaye kudancin kasar Lebanon, ko Ansarullah ta ci gaba da rayuwa cikin takunkuman tattalin arzki na kasar saudia har abada.? Wanda ba zai yu ba.

Daga karshe Baghaei yace, chancellor na Jamus bai cancanci ya yi magana dangane abubuwan da suka shafi kare hakkin bil’adama ba, ko kuma ya yiwa wani nisiha dangane da wani abu mai kama da haka ba. Saboda yana da hannu a zubar da jinin falasinawa kimani 73,000 wanda HKI ta yi a gaza. Da sauran wurare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted