Sojojin Yemen Sun Kakkabo Jirgin Saman Saudiyya Samfurin F-15

Mai Magana da yawun sojojin kasar Yemen Janar Yahya Sari ya sanar da cewa sojojin kasar sun yi nasarar kakkabo jirgin yakin Saudiyya samfurin f-15
jirgin sama na yaki

Mai Magana da yawun sojojin kasar Yemen Janar Yahya Sari ya sanar da cewa sojojin kasar sun yi nasarar kakkabo jirgin yakin Saudiyya samfurin f-15 wanda ya kai hari a gundumar “Ma’arib”.

Janar Sari ya kuma ce, sojojin na Yemen sun yi amfani da ne da makaman da su ka kera a cikin gida wajen kakkabo jirgin kirar Amurka.

Bugu da kari sojojin na Yemen sun tilasta wa wasu jiragen saman Saudiyya biyu na “F-15” da Typhon wajen barin samaniyar “ma’arib”.

 A gefe daya wani jami’in kasar Saudiyya Abdussalam ya bayyana cewa; Abinda ya faru yana nuni ne da yadda Yemen take kara karfi, don haka keta hurumin sararin samaniyar  Yemen ba zai zama abu mai sauki ba.

Haka nan kuma ya ce; Daga yanzu ya kamata matukan jiragen yakin Saudiyya da su yi tunanin cewa da Zarar sun taso daga sansaninsu to ba dole ne su sake komawa a raye gida ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted