Search
Close this search box.

Wani Likita Yana Iyo A Ciki Ambaliyar Ruwa A Sudan Domin Ceto Marasa Lafiya

An samu wani likita a Sudan mai kishin al’umma da sai ya yi iyo a cikin ruwa domin zuwa wajen aiki don ceton al’umma Rahotonni

An samu wani likita a Sudan mai kishin al’umma da sai ya yi iyo a cikin ruwa domin zuwa wajen aiki don ceton al’umma

Rahotonni sun bayyana cewa: Daraktan Asibitin Tokar da ke kasar Sudan, Dakta Mudassir Ahmed, ya kalubalanci babbar ambaliyar ruwa da ta mamaye garinsu da ke shiyar gabashin kasar, ta hanyar dagewa wajen cigaba da gudanar da aikinsa domin ceto marasa lafiya.

Babban lamari da ke yawo a kan shafukan sada zumunta shi ne yadda aka dauki hoton wani likita da ke yin iyo a cikin ambaliyar ruwa don isa asibiti domin gudanar da ayyukan ceto ga al’umma.

Dakta Mudassir ya shaida wa gidan talabijin na Al Jazeera cewa ya yi mamakin yadda aka dauki faifan bidiyonsa kuma a watsa a shafukan sada zumunta a duk lokacin da yake shiga cikin ruwa domin yin iyo zuwa asibiti don gudanar da ayuukan ceto.

Yana mai bayyana yadda lamarin ya faru da ya ce: Saboda katsewar ayyukan sadarwa, ya zama dole a je a kira shugaban sashen kula da mata masu juna biyu domin yi wa wata mace tiyatar gaggawa ta caesarean, kuma duk da kalubalen da ake fuskanta, suna godiyan Allah ayyukan sun yi nasara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments