Wani dan majalisar dokoki a nan Iran ya bukaci kasashen duniya su yi watsi da bambance bambance da ke tsakanin mutane a duniya, su kuma hada kai don ganin cewa an kori HKI a wasannin Olympic wadanda za’a gudanar a birnin Paris na kasar Faransa.
Kamfanin dillancin labaran Mehr na kasar Iran ya nakalto Muhammad Haasan Aasifari wakilin mai wakiltan mutanen Arak na tsakiyar kasar Iran yana fadar haka, ya kuma kara da cewa bayan da kasar Rasha ta farwa kasar Ukraine da yaki a shekara ta 2022 hukumomin wasannan daban daban a duniya musamman a kasashen turai sun haramtawa kasar Rasha da kuma kama kasar Belerus halattar duk wasannan da hukumomin suke gudanarwa, banda haka sun hana a gudanar da wasanni a wadannan kasashe.
Aasifari ya kammala da cewa yakamata kasashen duniya, su hada kai su kuma akuda duk wani bambance bambance da ke tsakaninsu don ganin hukumar wasannin Plympic ta kori yanwasan HKI halattar gasannin Olympic wadanda za’a gudanar a kasar Faransa nan gaba.
Ya ce, idan da gaske ne gwamnatin kasashen yamma suke yi na kare hakkin bil,adama to kuwa baikamata su bar hKI ta shiga cikin wasannan Olympic na kasar Faransa ba saboda kissan kiyashin da take aikatawa a kan al-ummar Falasdinu a gaza.