Kafafen watsa labarun Pakistan sun bayar da labarin cewa, wani dan kunar bakin wake a yankin Baluchistan ya kashe mutane 5 sannan kuma ya jikkata wasu 56.
Wannan harin na kunar bakin waken wata kungiya ce ta “Yanto Da Baluchistan” ta kai shi akan jami’an tsaron kasar ta Pakistan.
Wasu Karin sojojin 5 daga cikin wadanda su ka jikkata suna cikin halin rai kwakwai mutum kwakwai kamar yadda majiyar ta Pakistan ta ambata.
An kai wannan harin ne dai a lokacin da kasar ta Pakistan take fuskantar matsalolin tsaro, musamman ma dai a yankin Baluchestan dake da ‘yan aware.
A cikin shekarar da ta kare ta 2024 kadai an kashe mutanen da sun kai 782 a cikin wannan yankin.