Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa: Gwamnatin ‘yan Sahayoniyya ta kashe Falasdinawa sama da 150 a Gaza a watan da ya gabata
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a ranar Litinin cewa: Sama da Falasdinawa 150 ne aka kashe a hare-haren da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a yankin Gaza a watan Yuli, wanda shi ne adadi mafi girma na wata-wata tun farkon wannan shekarar.
Farhan Haq, Mataimakin Kakakin babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya ce: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare ta sama, harba manyan bindigogi da kuma harbe-harben bindiga a Gaza a karshen mako, wanda ya haifar da mutuwar fararen hula, ciki har da kananan yara.
A yayin wani taron manema labarai a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York, Haq, wanda ya ambaci bayanai daga Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu, ya bayar da rahoton mutuwar sama da Falasdinawa 150 a watan da ya gabata. Ya bayyana cewa mafi yawan hare-haren sun faru ne a yammacin yankin Gaza, inda mafi yawan al’ummar da ke zaune a wajen suka kai kusan miliyan 2.1.
Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta rubuta mutuwar Falasdinawa 152 a ranar Asabar da ta gabata, inda ta lura cewa wannan shi ne adadin mace-macen da aka samu a kowane wata tun farkon wannan shekarar.