Ruwa Ya Ci Rayukan Mutane 14 A Habasha

Kamfanin dillancin labarun AFP ya nakalto cewa a kalla mutane 14 ne su ka mutu yayin da wasu 5 su ka jikkata a wata cibiyar addini a Arewacin gundunar Amhara ta kasar Habasha.
Saudiyya Na Nazarin Kaucewa Fada Da Ansarullah Na Yemen

Kafar labaru ta Bloomberg ta ce; Saudiyya tana kokarin kaucewa fadada fada da Ansarullah na kasar Yemen bayan da Amurka ta ba ta shawarar kaucewa hakan. Majiyar ta kuma kara da cewa; Tare da cewa Saudiyya tana daura damarar yaki,amma a lokaci daya ta bude kafar tattaunawar diplomasiyya da Ansarullah ta hanyar kasar Oman.” Amurkan […]
Reuters: Makaman Amurka Masu Cin Dogon Zango Sun Kare A Yaki Da Iran

Majiyar kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya bayar da labarun cewa; Sojojin Amurka sun cinye mafi yawancin makamai masu linzami dake cin dogon zango da suke da su a tsawon lokacin yaki da Iran.” Rahoton na kamfanin dillancin Reuters ya kuma ambato majiyar sojan na Amurka tana cewa; Halin da ake ciki ya jefa tsoro a […]
Sheikh Kassim: Gwgawarmaya Za Ta Ci Gaba Matukar Da Akwai Mamaya

Har ila yau babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya ce; Mun yi Imani da Lebanon a matsayin kasa daya dunkulalliya wacce babu yadda za a iya raba ta, ko kuma a yi sassauci akan taku daya nata.”
Pezeshkian: Iran Ba Ta Neman Tada Hankali A Yankin

Pezeshkian ya bayyana a jiya Litinin, 12 ga watan Agusta cewa: “Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta son kara tada rikici ko kawo cikas ga tsaro a yankin, amma za ta kare tsaronta, muradun kasa, da kuma cikakken ikon yankinta da dukkan karfinta.”
Iran Da Saudiyya Sun Tattauna Kan Batutuwan Yankin

Bangarorin biyu sun tattauna sabbin abubuwan da suka faru a baya-bayan nan dangane da halin da ake ciki a yanzu, da kuma kokarin diflomasiyya na rage tashin hankali.
Araqchi Ya Tattauna Da Takwarorinsa Na Pakistan Da Oman

Ministan Harkokin Wajen Iran ya gudanar da tattaunawa ta wayar tarho da ministocin harkokin wajen kasashen Pakistan da Oman Ministan Harkokin Wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya yi tattaunawa daban-daban da takwarorinsa na Pakistan da kuma na Masarautar Oman. Mataimakin Fira Minista kuma Ministan Harkokin Wajen Pakistan Mohammad Ishaq Dar ya yi magana ta wayar […]
Ibnu Ridha: Kasar Iran Ba Ta Yarda Da Amurka Ba

Mukaddashin Ministan Tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Ba su yarda da Amurka ba… Duk wata karya yarjejeniya zasu mayar da martanin da ta dace Mukaddashin Ministan Tsaron Iran Birgediya Janar Majid Ibn Reza, a wata tattaunawa ta wayar tarho da Ministan Tsaron Turkiyya Yaşar Güler, ya jaddada wajibcin kafa tsarin tsaro na haɗin gwiwa […]
UN: Falasdinawa 150 Ne Isra’ila Ta Kashe Cikin Wata Guda A Gaza

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa: Gwamnatin ‘yan Sahayoniyya ta kashe Falasdinawa sama da 150 a Gaza a watan da ya gabata Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a ranar Litinin cewa: Sama da Falasdinawa 150 ne aka kashe a hare-haren da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a yankin Gaza a watan Yuli, wanda […]