Kungiyar harka islamiya IMN a tarayyar Najeriya ta gudanar da tattakin 40 na Imam Al-Hussain(a) a birnin Abuja na tarayyar kasar. Kuma sun mabiya kungiyar sun fiffito daga garuruwa da kauyuka gewaye da birnin don tunawa da cika kwanaki 40 da kissan Imam Al-Hussain(a) jikan manzon All..(s) a shekara ta 61 bayan hijira.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar iran a ranar litinin ce aka gudanar da tattakin wanda ya hada dubban daruruwan magoya bayan kungiyar daga ciki da kuma wajen Abuja saboda tunawa da wannan babban rana.
Shugaban harka Islamiyya sheikh Ibrahim El-Zagzagi ne ya yi jawabi na karshe a karshen taron na 40. An gudanar da irin wannan tarurrukan a garuruwa da dama a kasar. Hakama wasu kungiyoyi mabiya mazhabar iyalan gidan manzon All..(s) sun gudanar da tarurrukansu na 40 a cikin makaranyunsu ko wasu wuraren tarurruka a garuruwansu.