11-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Al-adu da ci gaban addini addinin musulunci a tarihi, wanda ni tahir amin yake kawo mako sau guda a ko wani mako. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.
///… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun tsaya inda muka yi magana dangane da yanda samun wadatuwar takarda a cikin al-ummar musulmi ya taimaka wajen kyautata karatu da karantarwa, da kuma yaduwar ilmi.
Har’ila yau mun bayyana cewa, addinin musulunci tun farkon bayyanarsa ya kwadaitar da musulmi karatu, tunda aya ta farko wacce ta sauka ga manzon All..(s) tana umurni da karatu ne, sannan All..ya kodaitar da musulmi su rubuta basussuka da suke bayarwa a tsakaninsu don kada a manta da hakkin wanda ya bayar da bashi ko da wani abu zai faru da wanda ya karbi bashin.
Dangane da ilmi, mun kawo hadisi inda manzon All..(s) yake magana kan cewa, mu daure ilmi da rubutu, ya sanya fansar wasu daga cikin fursinonin Badar koyawa yaran madina rubutu da karatu. Da wasu Misalai da dama.
Har’ila yau mun bayyana cewa, bayan wafatin manzon All..(s) da shekarun da basu fi 50 aka fara amfani da amfani da rubutu sosai a cikin musulmi, babu wanda aka rubuta maganarsa, ko kuma ya yada ilmin addini da duniya kamar Aliyu dan Abitalib (a), wanda dama shi ne kofar ilmin manzon All..(s).
An tattara mafi yawan khudubobinsa, wasikunsa, kalamansa a cikin lokacinda ya sami damar jagorancin al-ummar musulmi na kimani shekaru 5, inda aka tattara wasu daga cikinsu cikin littafin Nahjul Balagha wanda yake hannun musulmi a halin yanzu.
Daga karshe mun bayyana cewa zuwa zamanin Sarki Mansur Dawaniki daya daga cikin sarakunan Abbasiyawa, takardu da abin rubutu sun wadata a cikin musulmi, wanda ya kaiga wasu musulmin suna shigo da takardu daga kasar China a lokacin, sannan wasun ma, suna da masana’antun samar da takardu a cikin kasashen musulmi.
Wannan ya bude kofar tarjamar ilmi daga wasu kasashen da ba musulmi ba zuwa harshen larabci, sannan aka sami damar bunkasa ilmi na addini da duniya, kamar falsafa, da likitanci, da fannonin ilmin kimiyar lissafi da kimiyyar sanadarai da sauransu, wanda mun yi ishara garesu a cikin shirye-shiryemmu da suka gabata. A lokacin ne daular musulunci ta zama, cibiyar ilmi da bunkasa shi a duniya gaba dayanta.
Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa, kasashen musulmi sun wadatu da takardu ne bayan yake yake fatahin da suka yi bayan kogin furat na kasar Iraki.
Thalabi daya daga cikin malaman musulmi a karni na 11, yana cewa a shekara 134 daya daga cikin kwamandojin sojojin sarakunan Abbasiyawa mai suna Ziyad dan Saleh ya shiga yaki da sarakunan turkawa da kuma mutanen China a kusa da kogin Taraz a kasar da ake Turkistan daga baya. Ya sami nasara a kansu, sai ya kama wasu yan kasar China wadanda suka iya aikin samar da takardu, sai ya zo da su Samarakanda babban birnin Yankin. Daga nan sai suka kafa masana’antar takardu a birnin samaranda. Daga nan sana’ar samar da takardu ta watsu cikin kasashen musulmi.
Tha’alabi ya kara da cewa, saboda kyawu da kuma saukin farashin takardu na samarakanda a kasashen musulmi a lokacin, kowa na yabon takardun. Don haka musulmi sun koyi aikin samar da takardu ne daga hannun mutanen China a lokacin.
A lokacinda suna samarda takardu daga awduga da kuwa wasu tsirran. Don haka tun lokacin ne ake samar da takardu nau’ii daban daban a kasashen musulmi.
Sai kuma Ibn Nadim a cikin littafin Fehrest ya ambaci sunayen mutane da dama wadanda suke samar da takardun rubutu nau’i daban daban.
Bayan haka samar da takardu ya yadu zuwa kasashen Iraki, Sham, arewacin Afrika, Andulos (Espania a halin yanzu) da kuma Iran.
Daga karshe daya daga cikin waziran Sarki Haruna Rasheed daya daga cikin sarakunan Abbasiyawa wanda ake kira Fadlu dan Yahya Barmaki, ya samar da masana’antar takarda a birnin Bagdaza babban birnin Daular musulunci a lokacin.
A hankali takardun bagdaza suka yadu a cikin kasashen musulmi ya kuma sami shuhra, har sai ya kai, Shihabuddeen Qaqshandi yana cewa, saboda kyawun takardun bagadaza, ana kebesu don rubutun Al-kur’ani mai girma ko kuma wasu abubuwa masu muhimmanci.
A cikin karni na biyar qamariyya, sana’ar samar da takardu ya kai kasar Sham, kamar yanda Nasir Khusru a cikin littafin tafiyarsa (Safar Nomeh) yana cewa, a cikin birnin Tripoli na arewacin kasar Lebanon ana samarda takartun rubutu a cikin birnin wanda ya fi takartun samakanda kyau. Hakama a Damashk, ana samarda da takardun rubutu mafi kyau da na samarakanda. Wadannan takardun ana fitar da su zuwa gabacin Turai a lokacin.
Sannan daga areawacin Afrika ma kamfanonin samar da takardu suna fitar da takardun zuwa kasashen turai daga arewacin tekun medeteranian. A cikin kasar Iran kuma a cikin farkon karni na 7, mutanen garin Khonj kusa da garin Zanjon sun fara samar da takardu.
Bayan haka ne aka kafa kamfanin samarda takarda ta farko a kasashen Turai, a kuma kasar Italia, wato a shekara 1276 miladiyya. Sai kuma a kasar Faransa a shekara ta 1348 miladiyya sannan a kasar Jamus a shekara 1390 miladiyya, sannan kasar Jamusa a shekara 1348 sannan daga karshe kasar Ingila a shekara 1495 miladiyya.
A zamanin bayyanar addinin musulunci, kasashen Indiya, Iran da kuma Girka suna da ci gaba dai dai da zamaninsu, don haka wannan ci gaban ya shiga cikin ci gaban da musulmi suka samar daga baya.
Don haka daga wadan nan kasashe uku, kasar Girka, an tarjama ilmin mai bunkasa hankali, kamar mandiki da falsafa. Musulmi wadanda harshen ilminsu shi ne larabci sun amfana da wadanda ilmi ne ta hanyar tarjamasu daga harshen Girka, ko Siryani ko kuma Lateni, wadanda suka tarjama wadannan ilmomi mafi yawa kiristoci ne a kasar Iraki, da shamomi, wato Siriya turkiyya, Falasdinu Lebanon da Jordan ne. Musamman daga garin Harran wanda yake cikin yankin Urfa na kudancin kasar Turkiyya a halin yanzu.
Wadannan mutane da suka tarjama ilmin wadannan kasashe, dama kiristoci ne da suka musulunta, ko kuma saboda kyaututtukan da suke samu daga hannun sarakunan musulmi a lokacin.
Wani bangare mai yawa na ilmin girka an tarjamasu ne daga makarantar iskandariyya na kasar Masar, wacce itace mafi girma daga cikin cibiyoyin ilmin addinin kirista a lokacin. Kuma an tarjama ilmomin lissafi, taurari, likitanci da ilmin dabi’a daga wannan babban makarantar Girka. Ta cikin littafan da aka tarjama ne musulmi, suka san lissafin Batlimyus na kasar Masar wanda ya kware a ilmin taurari, da kuma taswiran duniya, da kuma ilmin geographia.
Banda wannan ta hanyar tarjama ne musulmi suka san likitocin girka, musamman littafan Jolinus da Baqraat, suka sami littafin Jabir dangane da guba da sauransu.
A cikin rabin karnin na biyu musulmi suka san manya manyan malamai, kamar su Aflatun, Fithagurth, Arosto.
Kafin haka sun san ilmin likitanci daga likitocin da suke zuwa kasar Sham. Bayan da Mu’awiya ya kwace khalifanci zuwa Damashq, likitoci da dama daga kasar Girka sun shigo birnin Demashq don neman aiki.
Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa Mu’awiya ya sami likita na musamman daga kasar Girka mai suna Othaar yana kula da lafiyarsa. Wani likita kirista mai suna Abul-Hakam ya ci gaba da kula da lafiyar Mu’awiya, sannan dangin Abul-Hakam sun ci gaba da ayyukan kula da lafiyan khalifofin musulmi daga umayyawa zuwa Abbasiyawa har zuwa farkon rabin karni na uku. Sun ce tsakanin karni na farko zuwa karni na uku ilmin ayyukan likitanci gaba daya, daga kasar girka ya koma cikin kasashen musulmi.
A wannan fagen wani matashi likita mai suna Hunain dan Ishak wanda a lokacin bai fi shekara 18 a duniya ba, ya tarjama littafan Jolinus kimani 100 kafin karshen rayuwarsa. Sai dai muna iya cewa hakan ya faru ne tare da kokarinsa da na dalibansa.
A dai dai wannan lokacin ne aka tarjama littafin Dioscorides danga ne da ilmin tsirrai. Wannan littafin yana da matukar muhimmanci a wajen mutanen girka a wannan fannin. Amma daga baya masana musulmi sun gudanar da bincike mai yawa sun kammala gani wasu ayyukan da ba’a kammala ba. Tare da wadan nan ayyukan tarjama da kuma karin bincike ne musulmi suka kai wani matsayi na sanin ilmin likitanci.
Wasu daga cikin ilmin kuma sun zowa al-ummar musulmi ne ta kasar India. A zamanin sarakunan Abbasiyawa ne dangantaka tsakanin kasar Indiya da musulmi ya fara karfi, kuma tun lokacin ne aka fara tarjamar fannonin ilmi daban daban , wadanda suka hada da ilmin likitanci da taurari da sauransu zuwa harshen larabci.
Aldomieli wani marubuci dan kasar Italiya, ya bayyana cewa, ilmomi da dama daga kasar India sun kaura daga kasar india zuwa kasashen musulmi, daga cikinsu har da ilmin da Abu Raihan Biruni ya bunkasa dangane da kasar India. Wadanda suka hada da ilmin likitanci, lissafi, da taurari. Duk sun hadu sun kawo ci gaba a kasashen musulmi a lokacin.