Ministan masana’antu, ma’adinai da kuma kasuwanci na kasar Iran ya gana da tokwaransa na kasar Pakistan inda bangarorin biyu suka tattauna dangane fadada harkokin makamashi tsakanin kasashen biyu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar tawagar ministan zuwa birnin Islamabad tana cewa, ministocin sun gana ne bayan taron kwamitin kasuwanci tsakanin kasashen biyu karo na 10TH a birnin Islamabad, da kuma ganawar ministan da majalisar dokokin kasar Pakistan a yau Laraba.
Labarin ya kara da cewa, bangarorin biyu, da farko sun yi bitan yarjeniyoyin da suka cimma a tsakaninsu a baya, musamman wadanda suka shafi man fetur gas da kuma sinadaran man fetur. Sun kuma tattauna dangane da zuba jari da kuma taimakawa juna a bangarorin gina masana’antu gwargwadon bukatun ko wace kasa.
Banda haka sun tattauna kan matsalolin da suka hana aiwatar da wasu yarjeniyoyin da suka cimma a tsakaninsu. Musamman a bangaren makamashi.
Kafin haka dai akwai yarjeniyar shimfida bututun gas daga kasar iran zuwa kasar Pakistan wanda gwamnatin amurka take adawa da shirin, kuma har yanzun shuwagabannin kasar Pakistan sun kasa gamsar da Amurka na a ci gaba da wannan shirin.
A bangaren Iran dai ta kammala shimfida bututun iskar gas wanda zai kaiwa Pakistan gas daga kasar har zuwa kan iyakar kasashen biyu amma kasar Pakistan ta kasa kammala nata bangaren saboda rashin amincewar Amurka.