Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ta Sanar Da Halakar Sojojinta 2 A Kudancin Kasar Lebanon

An Halaka Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila 2 A Kudancin Kasar Lebanon

Kafafen yada labarai na HKI sun tabbatar da halakar sojojin su guda biyu a kudancin kasar Lebanon da kuma raunata wasu kimani 7 a yau Laraba.

Tashar talabijan ta Aljazeera ta kasar ta kara da cewa majiyar yahudawan ta kara da cewa, sojojin yahudawan sun halaka ne a cikin wani gina a garin Majdal Zun dake kudancin kasar Lebanon inda dakarun kungiyar Hizbullah sun rika sun dana boma boma a cikinsa.

Labarin ya kara da cewa sojojin da suka halaka daga runduna ta 55 na sojojin Haramtacciyar kasar sannan ana aikin tiyata don kubutar da ran daya daga cikin wadanda suka ji rauni a asbitin Rambam da ke garin Haifa da aka mamaye. Wannan yana faruwa a dai dai lokacinda jiragen yakin yahudawan suke ci gaba da luguden wata a kan wasu wurare a kudancin kasar ta Lebanon, suna rusa gidaje suna kuma harbi kan garuruwa da makaman igwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted